Kanal O. Obasanjo bayan kammala yakin basasar Najeriya
Olusegun Obasanjo a shekara ta 2014.
Lokacin da Obasanjo na mulkin soja
mutum mutumi na obasanjo
obasanjo Yayin fa yake aikin soja
Olusegun Obasanjo tsohon Janar din soja, ɗan siyasan Nijeriya. An haife Obasanjo a shekara ta 1937 a birnin Abeokuta, Kudancin Najeriya (a yau itace jihar Ogun.
Lokacin da Obasanjo ya shiga harkokin siyasa
Olusegun Obasanjo shugaban kasar Nijeriya ne daga watan Fabrairu na shekarar 1976 zuwa Satumba shekara ta 1979 bayan mulikin Murtala Mohammed sannan ya mika wa Shehu Shagari) mulki bayan wa'adin mulkinsa na farko. Daga bisani Obasanjo ya sake zama shugaban kasar Nijeriya yayin da mulkin kasar yakoma kan turbar dimokaradiya, inda yashiga zabe a karkashin jamiyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma yasamu nasara aka rantsar dashi a watan Mayu shekarar 1999, sannan yasake samun shugabantar kasar akaro na biyu karkashin domokaradiya bayan ya sake cin zabe a shekara ta 2003. Karshen mulkinsa yakare a shekara ta 2007 inda yamara wa Umaru Musa Yar'adua baya kuma Yar'adua ya samu nasarar shugaban tar kasar. Daga shekara 2007.